Isa ga babban shafi
Wasanni

An dakatar da Mourinho daga halartar wasanni biyu saboda rashin da'a

An dakatar da Jose Mourinho daga halartar wasanni biyu, bayan da a ranar Talata alkalin wasa ya bashi jan kati saboda bacin ran da kocin ya nuna yayin wasan da AS Roma ta yi da Verona a gasar Seria A.

Jose Mourinho.
Jose Mourinho. REUTERS/Russell Cheyne
Talla

Mourinho ya yi wa alkalin wasa Luca Pairetto ihu, tare da kwaikwayon kiran wayar da aka yi masa, abin da ya kai ga ba shi jan kati.

Kafofin yada labaran Italiya sun ruwaito cewa Mourinho bai ji dadin yadda aka kara lokaci kadan ba a ranar Asabar, yayin wasan da aka tashi 2-2 tsakanin kungiyarsa ta AS Roma da Verona.

A yanzu Roma ta koma tazarar maki shida tsakaninta da Juventus wadda ke matsayi na hudu a gasar zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.