Isa ga babban shafi
Wasanni

Barcelona ta koma Europa bayan buga wasanni 191 a gasar Zakarun Turai

Bayan buga wasanni 191 a gasar Zakarun Turai a cikin shekaru 18 da suka gabata, a karon farko kungiyar Barcelona ta koma buga Europa, tun bayan da aka sakewa gasar suna.

Dan wasan gaba na kungiyar Barcelona Ansu Fati.
Dan wasan gaba na kungiyar Barcelona Ansu Fati. - AFP
Talla

Lokaci na karshe da Barcelona ta fafata gasar Europa wadda a baya ake kira da UEFA Cup shi ne kakar wasa ta 2003/2004, lokacin da Celtic ta fitar da ita daga gasar Zakarun Turai ta Champions League a zagaye na biyu da ya kunshi kungiyoyi 16.

Sau daya ne dai kawai FC Barcelona da Napoli suka taba karawa a wata babbar gasa, kuma hakan ya kasance ne shekaru biyu da suka gabata, a gasar Zakarun Turai ta kakar shekarar 2019 da 2020.

A zagayen farko na fafatawar ad suka yi, kungiyoyin sun tashi kunnen doki 1-1 a watan Fabrairu, sannan bayan dawowa daga hutun tilas na annobar Korona, suka kae karawa a zango na biyu cikin watan Agusta inda Barcelona ta tsallake zuwa zagayen kwata final, bayan lallasa Napolin da 3-1 a Spain.

Lionel Messi yayin karawar Barcelona da Napoli a kakar wasa ta shekarar 2019/2020.
Lionel Messi yayin karawar Barcelona da Napoli a kakar wasa ta shekarar 2019/2020. © Enric Fontcuberta/EPA

Sai dai fa a shekarun bayan wadannan kungiyoyi sun taba fafatawa har sau 5 a wasannin sada zumunci, kuma sau daya kawai Barcelona ta yi rashin nasara.

Wasan sada zumunci na farko da aka fafata shi ne na  ranar 25 ga watan Mayu cikin shekarar 1978 a birnin Naples, wanda aka tashi kunnen doki 1-1 tsakanin Napoli da Barcelona.

Ranar 22 ga watan Agusta kuma a 2011, Barcelona ta lallasa Napoli da kwallaye 5-0 a filin wasanta na Camp Nou.

Amma a shekarar 2014, ranar 6 ga watan Agusta, Napoli ce ta doke Barcelona da 1-0 a wasan sada zumuncin da suka buga a birnin Geneva.

Ranar 7 ga watan Agusta kuma cikin shekarar 2019 a birnin Miami, Barcelona ta doke Napoli da 2-1. A dai shekarar ta 2019, a ranar 10 ga watan na Agusta amma a birnin Michigan Barcelona ta lallasa Napoli da 4-0.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.