Isa ga babban shafi
Wasanni -Tennis

Nadal na daf da kafa tarihi a Australian Open

Rafael Nadal na iya kafa tarihi  na zama na farko da ya lashe babban kofin grand slam har sau 21 matsawar ya doke dan kasar Italiya, Matteo Berrettini a haduwar da za su yi anjima a yau Juma’a a wasan kusa da karshe na gasar Australian Open.

Rafael Nadal na daf da kafa tarihi a gasar Australian Open.
Rafael Nadal na daf da kafa tarihi a gasar Australian Open. Martin KEEP AFP
Talla

Lamba 2 a duniya a wasan tennis, Daniil Medvedev da  dan kasar Girka, lamba 4 a duniya, Stefanos Tsitsipas za su sabanta hamayyarsu a wani wasa mai kama da maimaicin haduwarsu ta baya a Melbourne, inda Medvedev ya samu nasara, wato za su barje gumi a a daren Juma’a a Melbourne Park.

Saura nasarori 2 dan kasar Spain din mai shekaru 35 ya zarce Novak Djokovic da Roger Federer a kokarin kasancewa dan wasan tennis da ya fi kowa samun nasarori a ajin maza.

Lamba na 7 a kwallon tennis a duniya, Berrettini,  mai shekaru 25, shine dan kasar Italiya na farko da ya taba zuwa matakin kusa da karshe a gasar Australian Open.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.