Isa ga babban shafi
Wasanni

Kungiyoyin Turai 10 na takarar kulla yarjejeniya da Endrick de Sousa

Manyan kungiyoyin kwallon kafa na nahiyar Turai da suka hada da Real Madrid, da Barcelona, ​​Atletico Madrid, Bayern Munich, PSG, Manchester United, Manchester City, Chelsea, Arsenal da kuma Liverpool sun shiga takarar neman kulla yarjejeniya da dan wasan gaba na kungiyar Palmeiras da ke kasar Brazil, Endrick Felipe Moreira de Sousa, mai shekaru 15.

Endrick Felipe Moreira de Sousa dan Brazil da ke wasa a kungiyar Palmeiras, wanda manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai guda 10 ke takara akansa.
Endrick Felipe Moreira de Sousa dan Brazil da ke wasa a kungiyar Palmeiras, wanda manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai guda 10 ke takara akansa. © Sportzwiki
Talla

Hotunan bidiyon da suka bayyana a watannin baya bayan nan, sun nuna yadda Endrick yayi fice wajen sarrafa tamaula a matakin matasa, inda ya ke da tarihin zura kwallo a raga, ciki har da wadda ya jefa a gasar Copinha, ta kungiyoyin 'yan kasa da shekaru 20 a Sao Paulo, wadda ta yi kama da irin kwallon da Cristiano Ronaldo ya jefa a ragar Juventus a gasar cin kofin zakarun Turai, lokacin da yake Spain.

Kungiyar ta Palmeiras ta dade tana fafutukar boye kwazon dan wasan nata gudun kada manyan kungiyoyi su yi gaggawar a raba ta dashi, tun bayan da ya zura  kwallaye biyar a wasanni uku na Copinha a cikin mintuna 90 kacal na lokacin wasan da ya samu.

Palmeiras dai na kara fuskantar matsin lamba daga kungiyoyin kasashen Turai a yayin da tuni Endrick ya kulla yarjejeniya da kamfanin Nike.

Euro miliyan 17 ne dai farashin kulla yarjejeniya da dan wasan a yanzu haka, amma kungiyar da ke wajen Brazil ba za ta iya daukarsa ba sai ya kai shekaru 18.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.