Isa ga babban shafi
Wasanni

Mai yiwuwa Barcelona ta tafka asarar makudan kudi akan gasar Zakarun Turai

Kungiyar Barcelona na fuskantar hatsarin tafka hasarar miliyoyin euro idan har ta yi rashin nasarar tsallakawa zuwa zagayen na biyu a gasar zakarun Turai yayin karawar ta Bayern Munich a Jamus.

Kocin kungiyar Barcelona Xavi Hernandez bayan rashin nasarar da suka yi a hannun Real Betis, ranar Asabar 4 ga watan Disamba.
Kocin kungiyar Barcelona Xavi Hernandez bayan rashin nasarar da suka yi a hannun Real Betis, ranar Asabar 4 ga watan Disamba. LLUIS GENE AFP/File
Talla

Barcelona ta tsinci kanta cikin tsaka mai wuya ce la’akari da cewar ita ce ta biyu a rukuni na 5 da maki 7,  maki 8 tsakaninta da Bayern Munich, sai dai kuma tsakaninta da ta 3 wato Benfica maki 2 ne kacal, wadda ita kuma za ta kara da Dynamo Kyiv, wasannin da dukkaninsu za a buga a ranar Laraba 8 ga watan Disamba.

Cikin kasafin kudinsu na kakar wasa ta bana, hukumar gudanarwar Barcelona ta tsara kasafin cewa za ta kai akalla zagayen kwata final a gasar Zakarun Turai, abinda ya sanya ficewarta daga gasar a matakin rukuni zai janyo mata hasarar euro miliyan 20 da dubu 200.

Sai dai kungiyar za ta iya rage hasarar idan ta yi kokarin lashe gasar Europar da take fuskantar hatasarin hantsilawa cikinta, domin idan ta dage kofin za ta lashe kyautar euro miliyan 14 da dubu 900.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.