Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Kwallon Ronaldo ta taimakawa Manchester United samun nasara kan Atalanta

Kwallon Cristiano Ronaldo ta karshe a wasan Manchester United da Atalanta ya taimakawa tawagar ta Ole Gunnar Solskjaer nasara tare da zamowa jagorar rukunin da ta ke na F da maki 6 karkashin gasar ta cin kofin zakarun Turai.

Kwallon Cristiano Ronaldo a wasansu da Atalanta.
Kwallon Cristiano Ronaldo a wasansu da Atalanta. Paul ELLIS AFP
Talla

Har zuwa tafiya hutun rabin lokaci Atalanta ke jagoranci da kwallaye biyu da banza kwallayen da ‘yan wasanta Mario Pasalic da kuma Merih Demiral na Turkiya suka zura mata tun a minti na 15 da kuma 29 da fara wasa.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne Marcus Rashford da taimakon Bruno Farnandes ya zurawa  Manchester United kwallonta na farko a minti na 53 gabanin kwallon Harry Maguire a minti 75 da ya bai wa kungiyar damar kunnen doki gabanin kwallon ta Ronaldo gab da karkare wasa.

A minti na 81 ne Ronaldo dan Portugal mai shekaru 36 ya zura kwallon tasa da kai, wadda ta zama kwallo ta 137 da ya zura karkashin gasar ta cin kofin zakarun Turai.

Da ya ke zantawa da manema labarai bayan tashi daga wasan Solskjaer ya ce abin da ya faru a wasan na jiya bai kamata ya baiwa mutane mamaki ba domin Manchester United ta saba makamanciyar nasarar.

Ko a makamancin wasan da ya gudana makwannin 3 da suka gabata tsakanin United da Villarreal kusan haka ne ya faru inda har zuwa hutun rabin lokaci Villarreal ke jagoranci da kwallo 1 da banza amma kuma bayan dawowa daga hutun rabin lokaci United ta bayar da mamakin nasara da kwallo 2 da 1 shi ma dai sakamakon kwallon da Ronaldo ya zura mata a wancan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.