Isa ga babban shafi
Wasanni

Real Madrid ta lallasa Shakhtar Donetsk da ci 5 - 0 a gasar zakarun Turai

Real Madrid ta lallasa Shakhtar Donetsk da ci 5-0 a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Talata yayin da Karim Benzema ya ci kwallo a jajibirin shari'ar da ake yi masa a Faransa bisa zargin hadin baki wajen bata suna.

Dan wasan gaba na Real Madrid Vinicius yayin wasansu da  Shakhtar Donetsk a gasar cin kofin zakarun turai, 19/10/21.
Dan wasan gaba na Real Madrid Vinicius yayin wasansu da Shakhtar Donetsk a gasar cin kofin zakarun turai, 19/10/21. Sergei SUPINSKY AFP
Talla

Dan wasan Donetsk Serhiy Kryvtsov ya ci gidansu kafin Vinicius Junior ya kara kwallaye biyu, Rodrygo ya ci na hudu. Sai kuma Benzema ya kara ta biyar ana daf da tashi wasa.

Da wannan sakamakon Real Madrid ta ci gaba da zama ta biyu a rukuni na hudu da maki shida, iri daya da na FC Sheriff, wadda ta sha kashi a gidan Inter Milan da ci 3-1.

A wannan Laraba ne dai dan wasan gaba na Faransa Karim Benzema da wasu mutane hudu ke gurfana kaban kuliya kan zarginsu da hannu a yunkurin bata ma wani tsohon abokin wasansa Mathieu Valbuena suna a shari'ar da aka sani da “faifayin lalata”. Sai dai babu tabbas ko Benzema zai kasance a shari’ar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.