Isa ga babban shafi
WASANNI

Za'a sanar da sunayen wadanda suka cancanci lashe kyautar Ballon d'Or

Masu shirya bata da kyautar Ballon d'Or da ake baiwa gwarzon dan kwallon kafar da ya yi fitce a shekara, sun ce za’a bada kyautar a ranar 29 ga Nuwamba a birnin Paris na kasar Faransa.

Kyautar Ballon d'Or da ake baiwa gwarzon kwallon kafar shekara da ake yi a Zurich, ranar 11 ga watan Janairun shekarar 2019.
Kyautar Ballon d'Or da ake baiwa gwarzon kwallon kafar shekara da ake yi a Zurich, ranar 11 ga watan Janairun shekarar 2019. AFP/Archives
Talla

Mujallar ta Faransa dake bada kyautar tace, a ranar 8 ga watan Oktoba za a bayyana sunayen wadanda za a zaba don basu da kyaututtukan, wadanda suka hada da gwarzon dan wasa na Maza da na Mata, da na bangaren matashin dan wasa da kuma golan da yayi fitce a shekara.

Lionel Messi da lashe kyautar har sau shida da Megan Rapinoe suka lashe lambobin yabon na ƙarshe s shekarar 2019.

An soke taron shekarar da ta gabata saboda barkewar cutar coronavirus.

Baya ga kyautar FIFA ta kwannan nan, Ballon d'Or, wanda Stanley Matthews ya fara karba a shekarar 1956, ya kasance ɗaya daga cikin kyaututtukan mafi girma da daraja a fannin wasannin ƙwallon ƙafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.