Isa ga babban shafi
Wasanni

Pulisic zai rasa wasar Chelsea da Arsenal saboda harbuwa da korona

Dan wasan gaba na Chelsea Chiristian Pulisic ya kamu da cutar Covid-19, lamarin da yasa bazai shiga daga fafatawar kungiyar sa da Arsenal ba a gasar Premier Ingila, kamar yadda Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya bayyana wannan Jumma'a.

Dan wasan gaba na Chelsea Chiristian Pulisic rike da kambin gasar European Super Cup da kungiyar sa ta dauka bayan doke Villarreal a watan Agustan 2021
Dan wasan gaba na Chelsea Chiristian Pulisic rike da kambin gasar European Super Cup da kungiyar sa ta dauka bayan doke Villarreal a watan Agustan 2021 Action Images via Reuters - JASON CAIRNDUFF
Talla

Dan wasan na Amurka bai samu halartar atisayen budewa na Chelsea na ranar Laraba ba, kuma baya cikin wasan ranar Lahadi a filin wasa na Emirates yayin da ya kebe kansa.

Amma Hakim Ziyech da N’Golo Kante duk sun koma filin atisaye, kuma zasu tabbatar da koshin lafiyarsu a wasan da kungiyoyin London 2 zasu fafata.

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta fara gasar Firimiyar bana da kafar dama, inda ta lallasa Crystal Palace da ci 3-0 a karshen makon da ya gabata a gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.