Rashford zai shafe makonni 12 yana jinya bayan tiyata
Dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford na iya rasa murza leda har zuwa karshen watan Oktoba bayan shawarar da ya yanke na yin tiyata kan raunin da ya samu a kafadarsa.
Wallafawa ranar:
Tuni Rashford, mai shekaru 23, yayi gwaje-gwajen da hotunan raunin ranar Talata bayan matsalar ta kawo masa cikas a tsakiyar kakar wasanni ta 2020 - 21.
An yanke shawarar yi masa tiyatar ce, bayan yanke kaunar cewa hutu kadai bazai iya magance raunin da ya samu ba, kamar yadda likitoci suka bayyana tun farko.
Ana hasashen Rashford zai shafe makwanni 12 yana jinya, wanda hakan zai kawo cikas ga shirin kocin United Ole Gunnar Solskjaer na fara sabon kakar cikin nasara.
Rashford ya ci kwallaye 11 a wasanni 37 da ya buga a gasar Firimiyar bara, amma bai takawa Ingila rawar gani ba a gasar Euro 2020 da aka kammala.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu