Isa ga babban shafi
Ingila-Kwallon Kafa

UEFA na tuhumar Ingila kan yadda 'yan daba suka yi barna a Wembley

Hukumar Kwallon Kafar Turai UEFA ta kaddamar da bincike kan yadda aka keta matakan tsaro a filin wasa na Wembley a fafatawar karshe ta Gasar Cin Kofin Kasashen Turai da aka kammala a karshen mako.

Magoya bayan Ingila a kofar harabar filin wasa na Wembley
Magoya bayan Ingila a kofar harabar filin wasa na Wembley Niklas HALLE'N AFP
Talla

Magoya bayan Ingila sun yi arangama da jami’an tsaro a yayin yunkurinsu na kutsawa cikin filin wasan a ranar Lahadin da ta gabata duk da cewa ba su sayi tikiti ba.

Magoya bayan na Ingila sun haddasa fitina tare da jefe-jefe da karikitai da kuma kunna wuta  mai tartsatsi, sannan suka rika ihu a yayin da Italiya ke rera taken kasarta gabanin soma wasan.

Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Ingila, Mark Bullingham ya nemi afuwar halastattun magoya bayan da suka sayi tikiti amma suka gaza shiga filin wasan saboda yadda ‘yan daba suka mamaye kujerunsu.

Yanzu haka Hukumar Kwallon Kafar Ingila ta FA za ta hada kai da jami’an tsaro domin haramta wa duk wanda aka samu da laifi halartar wasanni.

Ingila dai ta yi rashin nasara a hannun Italiya a bugun fanariti bayan sun yi canjarasa 1-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.