Isa ga babban shafi
Wasanni - Kwallon Kafa

Kanwar Emiliano Sala tayi yunkurin kashe kanta

Kanwar fitaccen dan wasan kungiyar Nantes Emiliano Salah mai suna Romina Sala na can kwance a wani asibiti dake kasar Argentina cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai, sakamakon kokarin kashe kanta da ta yi.

Romina Sala, kanwar fitaccen dan wasan kungiyar Nantes Emiliano Sala.
Romina Sala, kanwar fitaccen dan wasan kungiyar Nantes Emiliano Sala. © AFP/Getty Images
Talla

Kawo yanzu dai babu karin bayan kan dalilin da ya sanya Romina yunkurin halaka kan nata, wadda ta kasance mai magana da yawun iyalansu tun bayan mutuwar yayanta Emiliano Sala a watan Janairun shekarar 2019.

Hoton marigayi Emiliano Sala, a gaban filin wasa na kungiyar Nantes dake kasar Faransa.
Hoton marigayi Emiliano Sala, a gaban filin wasa na kungiyar Nantes dake kasar Faransa. AFP/Archivos

Salah ya rasa ransa ne dai sakamakon hatsarin da jirgin saman da yake ciki yayi, a lokacin da suke kan hanyar zuwa birnin Cardiff daga Nantes bayan sauyin shekar da yayi daga gasar Ligue 1 ta Faransa zuwa Firimiyar Ingila.

Bayan shafe makwanni a laluban baraguzan jirgin saman an gano gawar Sala a mashigin ruwan da ya sada Ingila da Faransa, sai dai har zuwa wannan lokaci ba a samu nasarar gano gawar direban jirgin ba, mai suna David Ibbotson.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.