Isa ga babban shafi
Wasanni - kwallon kafa

Kevin de Bruyne ya lashe kyautar PFA karo na biyu a jere

Dan wasan tsakiya na Manchester City, Kevin de Bruyne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar kungiyar kwararrun 'yan wasan Ingila ta bana ajin maza karo na biyu a jere.

Dan wasan Manchester City Kevin De Bruyne
Dan wasan Manchester City Kevin De Bruyne PETER POWELL POOL/AFP
Talla

Yayin da Phil Poden shima daga City ya lashe kyautar matashin da ba kamarsa a kakar gasar ingila da aka karkare. 

Dukkannin 'yan wasan biyu na daga cikin wadanda suka taka rawar gani a nasarar da Manchester City ta samu wajen lashe gasar Premier Ingila ta bana, kuma na uku cikin kaka hudu da kuma kofin Carabao.

Dan wasan Manchester City Kevin De Bruyne
Dan wasan Manchester City Kevin De Bruyne Dave Thompson POOL/AFP

Cristiano Ronaldo

De Bruyne, mai shekara 29, shi ne na biyu da ya lashe kyautar a jere, bayan Cristiano Ronaldo da ya nuna irin wannan bajintar a lokacin da yake taka leda a Manchester United.

Dan wasan na tawagar kwallon kafar Belgium, ya ci wa kungiyar kwallaye shida a gasar Premier, tare da taimakawa a ci kwallaye 12  a wannan kakar da aka kammala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.