Chelsea na neman tagulawa Madrid lissafi a gasar zakarun Turai
Chelsea ta sanya Real Madrid ta Zinédine Zidane cikin mawuyacin hali a fafatawar da sukayi daren jiya a Madrid babban birnin Spain, a matakin daf da na karshe haduwar farko na gasar neman cin kofin zakarun Turai bayan da aka Karkare wasa kunnen doki 1-1.
Wallafawa ranar:
Tawagar Thomas Tuchel ta fara zura kwallo mintu 14 da soma wasa ta hannun Pulisic Kristen kafin Karim Benzema ya farkewa Madrid kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Kwallo daya da aka zura mata a gida kafin tashi daya-daya, ya dagulawa tawagar Zidan lissafi, lamarin da zai kaisu ga buga wasa zagaye na biyu Stamford Bridge gidan Chealsea 5 ga wata Mayu cikin matsin lamba na dole sai tayi nasara.
Yanzu haka Pulisic ya zama dan Amurka na farko da ya taba cin kwallo a wasan daf da na karshe a gasar neman cin kofin zakarun nahiyar Turai Champions League, yayin da Karim Benzema ya ci kwallo na 71 a a gasar, abin da ya kaishi mataki na hudu a jerin wadanda suka nunan wannan bajintar, baya ga Cristiano Ronaldo da Lionel Messi da kuma Robert Lewandowski.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu