Isa ga babban shafi
Wasanni - Gasar Zakarun Turai

Tauraruwar Haaland na Dortmund na ci gaba da haskake Duniyar kwallo

Tauraruwar dan wasan Borussia Dortmund Erling Braut Haaland na ci gaba da haskawa yayinda farin jininsa ke ci gaba da kaure Duniyar kwallo ba kadai ga ‘yan kallo ba har tsakanin ‘yan wasa da kuma alkalan wasan.

Erling Haaland da ke taka leda a Borussia Dortmund.
Erling Haaland da ke taka leda a Borussia Dortmund. Ina Fassbender Pool/AFP/Archivos
Talla

Sai dai matakin alkalin wasa Ovidiu Hategan na neman Braut Haaland ya yi masa sa hannu, ya janyo cece-kuce da ya kai ga tafka muhawara akai.

Bayan kammala wasan na jiya wanda Dortmund ta sha kaye da kwallaye 2 da 1 dai anga yadda Hategan ya nufi Haaland tare da mika masa katina biyu don ya yi masa sa hannunsa, wanda ke nuna shi magoyi bayansa ne.

Tuni dai Hategan ya fara fuskantar caccaka daga masu sharhi wasanni, inda Owen Hargreaves tsohon dan wasan Manchester City ke ganin bai kamata alkalin wasan ya yi hakan a gaban sauran ‘yan wasa ba.

Sai dai Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola da ke fatan sayo Haaland a sabuwar kaka, ya ce da yiwuwar alkalin wasan ya nemi sa hannun ne saboda ‘ya’yansa magoya bayan Haaland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.