Isa ga babban shafi
Wasanni

City ta janye aniyar neman kulla yarjejeniya da Messi

Mai horas da Manchester City Pep Guardiola ya janye aniyar sa ta neman kulla yarjejeniya da kaftin din Barcelona Lionel Messi.

Kocin Manchester City Pep Guardiola.
Kocin Manchester City Pep Guardiola. AP - Mark Schiefelbein
Talla

Kafin matakin na kocin na City dai, a baya kungiyar ke kan gaba a tsakanin wadanda aka sa ran za su kulla yarjejeniya da Messi, idan ya rabu da Barcelona a karshen wannan kakar wasa.

Sai dai bayan yunkurin sauyin shekarar da yayi a bara, ga dukkanin alamu a yanzu haka Messi ya janye aniyarsa sakamakon farfadowar karsashin kungiyarsa da shi kansa a karkashin sabon kocinsu Ronald Koeman da kuma shugaban Barcelona Juan Laporta da ya sake darewa mukamin a karo na biyu.

A halin yanzu rahotanni sun ce a maimakon Messi kungiyar Manchester City za ta nemi kulla yarjejeniyar da ko dai Erling Haalanda, Romelu Lukaku, ko kuma Harry Kane, don maye gurbin dan wasanta Sergio Aguero da take shirin rabuwa da shi da zarar yarjejeniyarsa ta kare a karshen kakara wasa ta bana.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.