Kungiyar Juventus ta fice daga gasar cin kofin zakarun Turai na UEFA
A jiya Laraba an buga wasani tsakanin kungiyoyi na yankin Turai, wanda bayan haka ,wasu daga cikin kungiyoyi kama da Juventus suka yi bankwana da gasar ga baki daya.
Wallafawa ranar:
Duk da kokarin abokanin tafiyar Christiano Ronaldo a wannan fafatawa da kungiyar FC Porto, Juventus ta yi kasa a gwuiwa kuma indan aka yi tuni ranar 17 ga watan da ya gabata, wato Februrary a karawar farko da ta hada kungiyoyi biyu Fc Porto ta yi nasara da ci 2 da 1 a gida, sai kuma jiya a yayinda da ta bakuci Juventus ,kungiyar Juventus ta samu nasara da ci 3 da biyu, sai dai hakan bai baiwa kungiyar damar tsallakawa mataki na gaba, kasancewa ta samu rashin nasara a yayinda ta bakunci Fc Porto.
Da jimawa dai dan wasan kungiyar Christiano Ronaldo na daga cikin yan wasan dake ci gaba da fuskantar suka ko caccaka daga magabatan kungiyar ta Juventus dake yi masa kalon mutumin da ya gaza wajen ceto wannan kungiya tun bayan sayo sa daga Real Madrid.
Yanzu haka kalo ya koma bangaren magabatan kungiyar da shi dan wasan don sanar da matsayar su na ci gaba da taka leda da wannan kungiyar ta Juventus ko raba gari da kungiyar ga baki daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu