Bayern Munich ta lashe gasar kwararrun duniya
Bayern Munich ta lashe kofin Gasar Kwararrun Kungiyoyin Duniya da FIFA ke shiryawa bayan ta samu nasara da ci daya mai ban haushi kan Tigres ta Mexico a wasan karshe da suka fafata a kasar Qatar.
Wallafawa ranar:
Wannan shi ne kofi na shida da kungiyar Bayren Munich ta lashe a cikin watanni tara da suka hada da kofin Gasar Super Cup ta Turai da kuma wata gasar Super Cup din ta Jamus baya ga kofin Zakarun Nahiyar Turai da kungiyar ta lashe a kakar da ta gabata.
Benjamin Pavard ne ya ci wa Bayern Munich kwallon da ya tilo a karawarta da Tigres a minti na 59 a jiya.
Kungiyar ta Tigres ita ce ta farko daga yankin arewaci da tsakiyar Amurka da ta fara zuwa matakin wasan karshe a gasar ta kwararrun kungiyoyin duniya, amma ta gaza lashe kofin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu