Bayern Munich ta kama hanyar lashe gasar zakarun Turai
Bayern Munich ta kama hanyar lashe kofin zakarun Turai a bana bayan ta lallasa Lyon a wasan dab da na karshe da ci 3-0 a ranar Laraba, abin da ya ba ta damar tsallakawa zuwa matakin wasan karshe.
Wallafawa ranar:
A ranar Lahadi mai zuwa Bayern Munich ta Jamus za ta hadu da Paris Saint Germaine ta Faransa a wasan karshe na cin kofin zakarun Turai.
Kocin Bayern Munich, Hansi Flick ya bayyana cewa, akwai bukatar ‘yan wasansa su tamke tsaron bayansu a yayin karawarsu da PSG a wasan na karshe.
A bangare guda, Munich ta samu nasara a wasanni 10 jere da juna da ta buga a gasar ta cin kofin zakarun Turai, wato irin tarihin da Real Madrid ta kafa a shekarar 2015 a gasar, abin da ya sa masharhanta ke ganin cewa, watakila ta dage kofin zakarun Turai a bana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu