Isa ga babban shafi
Wasanni

Har yanzu akwai sauran aiki a gabanmu - Zidane

Mai horar da ‘yan wasan Real Madrid Zinadine Zidane yace babu hutu ga ‘yan wasan sa bayan buga wasan karshe na La Liga da za suyi gobe lahadi, saboda shirin mayar da hankali kan gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.

'Yan wasan Real Madrid tare da mai horas da su Zinedine Zidane bayan lashe kofin gasar La Liga karo na 34.
'Yan wasan Real Madrid tare da mai horas da su Zinedine Zidane bayan lashe kofin gasar La Liga karo na 34. AFP
Talla

Tuni dai Madrid suka lashe gasar La Liga ta bana sakamakon nasarar da suka samu a karawar da suka yi daren alhamis, wanda shine karo na 34 da kungiyar ke lashewa.

Kungiyar Madrid na kokarin ganin ta farke ci 2-1 da Manchester City ta mata a karawar da suka yi a gasar cin kofin zakarun Turai zagayen ‘yan 16.

Yayin ganawa da manema labarai yau asabar, Zidane yace bayan wasan gobe da zasu kara da Leganes, zasu dan huta kadan kafin cigaba da atisaye domin karawa da City saboda kakar bana bata kare ba sai an kammala gasar Turai.

Dangane da wasan gobe kuwa, Zidane yace babu sassauci domin zasu tinkare shi kamar yadda suka yiwa na baya.

Leganes na neman nasara a karawar gobe da za suyi da Madrid da kuma fatar ganin Celta Vigo ta sha kasha hannun Espanyol domin bata damar cigaba da zama a La Liga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.