Isa ga babban shafi
Wasanni

Kamfanin Najeriya ya fara daukar nauyin gasar Kenya

Kamfanin cacar yanar gizo na Najeriya Betking ya zama sabon mai daukar nauyin gasar firimiya lig ta kasar Kenya a karkashin wata hadaka ta zunzurutun kudi har Dala miliyan 11.

Betking na Najeriya ya zaman sabon mai daukar nauyin gasar firimiya ta Kenya
Betking na Najeriya ya zaman sabon mai daukar nauyin gasar firimiya ta Kenya AFP
Talla

Wannan hadakar za ta ci gaba da aiki har zuwa shekarar 2025 kamar yadda Hukumar Kwallon Kafar Kenya ta sanar a wannan Alhamis.

Hukumar ta ce, sabon daukar nauyin shi ne mafi girma da aka gani a tarihin kwallon kafa a kasar ta Kenya.

A karkashin hadakar, za a rika biyan kowane klub da ke taka leda a gasar lig din ta Kenya akalla Shilling miliyan 8 a kowacce shekara.

Wannan na zuwa ne a bayan kamfanin SportPesa ya janye daga daukar nauyin gasar ta Kenya a cikin watan Satumba sakamakon rikicin kudin haraji tsakaninsa da gwamnatin kasar.

Betking ya tsallaka zuwa Kenya ne a daidai lokacin da gasar firimiyar Najeriya ke fuskantar matsaloli da dama, ciki har da batun daukar nauyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.