Isa ga babban shafi
Wasanni

'Atletico Madrid ta ji tsoron karawa da Liverpool'

Kocin Liverpool Jurgen Kloop ya caccaki salon da Atletico Madrid ta yi amfani da shi wajen tsare bayanta a wasan da ya kawo karshen fafutukar Liverpool a gasar zakarun Turai ta bana.

Yayin karawa tsakanin Liverpool da Atletico Madrid a gasar zakarun Turai
Yayin karawa tsakanin Liverpool da Atletico Madrid a gasar zakarun Turai Reuters/Carl Recine
Talla

Atletico Madrid ta yi waje da Liverpool mai rike da kambin gasar bayan ta yi mata jumullar ci 4-2, idan aka hada da sakamakon wasansu zagayen farko.

Kloop ya gaza boye bacin ransa kan yadda Atletico ta samu nasara a kansu musamman ganin yadda kocinta, Diego Simeone ya tsara wa ‘yan wasan wani irin salon tsaron baya.

A cewar Kloop, sam bai gamsu da salon taka ledar Atletico Madrid ba domin sun tsaya ne kawai suna ta kare hare-haren kwallaye a maimakon su saki jiki a murza kwallon a kasa.

Sai dai a martanin da Simeone ya mayar ya ce, sun buga kwallo ne don samun nasara.

Da fari dai, an zaci Liverpool za ta samu nasara ganin yadda ta fara zura kwallaye biyu a wasan na ranar Laraba, amma daga bisani Atletico ta farke har ta kara ta uku bayan karin lokaci da aka yi musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.