Alkalin wasa bai kyauta mana ba - Conte
Kocin Inter Antonio Conte ya caccaki alkalin wasa, bayan doke tawagarsa 2-1 da Barcelona ta yi a jiya Laraba.
Wallafawa ranar:
Bayan dan wasan Inter Laurataro Martinez ya sanya kungiyarsa a gaba da kwallo daya da ya ci a cikin minti na biyu da fara wasa, Suarez ya ci kwallaye biyu bayan hutu, wasa ya tashi 2-1.
Amma Conte ya na ganin ba a mai adalci ba, don an wa tawagarsa coge.
Conte wanda ya sha kashedi daga alkalin wasa saboda yadda ya yi ta yin mazurai ga alkalin wasan, yana ganin kamata yayi a ba tawagarsa bugun daga – kai - sai – mai - tsaron raga lokacin da aka rafke dan wasan sa Stefano Sensi amma alkalin wasa ya dauke kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu