Isa ga babban shafi
wasanni

Ba za a mu yi amfani da fasahar alkalanci ba a Turai- Ceferin

Hukumar Kwallon Kafar nahiyar Turai ta ce, ba za ta yi amfani da fasahar bidiyon da ke taimaka wa alkalin wasa a kakar gasar zakarun Turai mai zuwa ba saboda tarin rudanin da ke tattare da fasahar kamar yadda shugaban hukumar, Aleksander Ceferin ya bayyana.

An kirkiri fasahar bidiyon alkalanci don taimaka wa alkalin wasa wajen yanke hukunci da kuma kauce wa kura-kurai
An kirkiri fasahar bidiyon alkalanci don taimaka wa alkalin wasa wajen yanke hukunci da kuma kauce wa kura-kurai FRANCK FIFE / AFP
Talla

Ceferin ya ce, kawo yanzu babu wanda ke da cikakkiyar masaniya kan yadda fasahar ke aiki saboda rudanin da ke cikinta.

Ceferin ya kara da cewa, lallai wannan fasahar tana da kyau amma kar a yi garajen fara amfani da ita.

Kalamansa na zuwa ne a yayin da da Kwamitin Kwallon Kafa na kasa da kasa ya gudanar da wani taro a ranar Asabar don yanke shawara game da amincewa da fasahar kafin aiki da ita a gasar cin kofin duniya a Rasha a bana.

An dai yi amfani da fasahar a wasu kasahe kamar Ingila a gasar firimiya da Carabao da kuma Jamus a gasar Bundesliga, sai kuma Italiya a gasar Serie A.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.