Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta iya lashe kofi kwallon kafa na Duniya a Rasha

Mai horar da kungiyar kwallon kafa na kasar Perou Ricardo Gareca ya bayyana cewa ya na da yakini cewa kungiyar kwallon kafar Faransa za ta taka gaggarumar rawa a gasar cin kofi kwallon kafar Duniya da za ta gudana a Rasha a shekarar 2018.

Sunayen kungiyoyi da za su jagoranci rukunoni a gasar cin kofin Duniya na Rasha  a 2018.
Sunayen kungiyoyi da za su jagoranci rukunoni a gasar cin kofin Duniya na Rasha a 2018. REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Ranar 16 ga watan yuni shekarar 2018 Faransa za ta karawar farko da Austria a filin wasa na Kazan.

Ranar 21 alhamis na watan yuni Faransa za ta fafata da kungiyar kwallon kafar Perou a filin wasa na Ekaterinbourg, sai wasar karshe tsakanin Danemark da Faransa ranar 26 ga watan yuni ranar talata na shekarar 2018 a filin wasa na birnin Moscou.

Sai da daya daga cikin yan wasan gaban kungiyar kwallon kafar Perou Paolo Guerrero dake taka leda a kulob na Grenade a Spain na fuskantar hukuncin dakatarwa daga kotun da’a na hukumar kwallon kafar Duniya ta Fifa da ta hakikanta cewa dan wasan ya yi amfani da kwayoyin dake kara kuzari ranar 20 ga watan yuli na shekarar 2016 a wata wasa da tsohon kulob din sa na Independante Valle ya buga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.