Barcelona na cikin tsaka mai wuya
Wasu daga cikin masu sharhi kan wasan kwallon kafa sun ce akwai aiki babba a gaban ‘yan wasan gaba na Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, wato Neymar, Suarez da kuma Messi wajen zurawa kungiyarsu kwallaye a ragar Juventus a ranar 19 ga watan Afrilu don kaiwa mataki na gaba a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai.
Wallafawa ranar:
Kungiyar Juventus ta lallasa Barcelona da 3-0 a zagayen farko na wasan da suka a buga a birnin Turin na Italiya a talatar da ta gabata, ta hannun ‘yan wasanta Dybala da ya zura kwallaye 2 da Giorgio Chiellini.
Tun bayan fara wgasar ta cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar turai, su biyu kawai aka samu nasarar jefawa kungiyar Juventus kwallo a raga.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu