Isa ga babban shafi
Wasanni-Afrika

Damar horar da kasar Afrika ta Kudu ta kufcewa Siasia

Tsohon kocin tawagar ‘yan wasan Najeriya ta Super Eagles Samson Siasia ya bayyana rashin jin dadinsa, kan yadda aka zare sunansa daga cikin wadanda ke neman a basu damar jan ragamar horar da tawagar ‘yan wasan Bafana Bafana ta kasar Afrika da Kudu.

Tsohon mai horar da tawagar 'yan wasan Super Eagles ta Najeriya Samson Siasia
Tsohon mai horar da tawagar 'yan wasan Super Eagles ta Najeriya Samson Siasia kwesesports
Talla

Wannan na zuwakwanaki kadan bayanda Siasia ya rasa damarsa a neman horar da kasar Rwanda.

Da fari dai Siasia ne kada mai horarwa bakar fata aka zaba tare da wasu guda bakawai da za’a tantance domin daukar guda aikin horar da Afrika ta Kudu, daga cikin guda 47 da suka nemi a basu wannan dama.

A halin yanzu dai, daga cikin wadanda suka rage da za’a tantance don horar da Africa ta Kudu, sun hadar da kocin Kamaru dan kasar Belgium Hugo Broos da ya jagoranci kasar lashe gasar cin kofin nahiyar afrika ta bana da aka kammala a Gabon, sai kuma mai horar da kasar Morocco dan Faransa, Herve Renard wanda ya taimakawa Zambia lashe kofin gasar cin kofin Afrika a shekara ta 2012.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.