Isa ga babban shafi
Premier

Lokacin da Leicester za ta lashe Firimiya

Leicester City ba ta taba lashe kofin gasar Firimiya ba ta ingila a tarihin kungiyar, amma Yanzu haka a bana ita ke jagorancin teburin gasar da tazarar maki 7 tsakaninta da Tottenham.

Manajan Leicester City Claudio Ranieri yana murna
Manajan Leicester City Claudio Ranieri yana murna REUTERS
Talla

Maki uku Leicester City ke nema a yanzu ta lashe kofin Firimiya a karon farko bayan Tottenham ta yi kunnen doki ci 1 da 1 da West Brom.

Hakan na nufin Leicester na iya bikin lashe kofin Premier a Old Trafford a ranar lahadi idan har ta doke Manchester United.

Idan kuma sakamakon bai yi wa Leicester dadi ba a Old Trafford, tana iya bikin lashe kofin Premier idan har Chelsea ta doke Tottenham.

A kakar da ta gabata saura kiris Leicester ta fice Firimiya, amma a bana Leicester ta ratso tsakanin manyan kungiyoyin Ingila ta dare teburin gasar a saman Manchester City da Arsenal da Manchester United da Liverpool da kuma Chelsea da ta lashe kofin a bara.

Leicester City dai mallakin wani attajiran kasar Thailand ne, kuma wannan ne karon farko da kungiyar ta tsallake zuwa gasar zakarun Turai.

Liecester ta taba zuwa matsayi na biyu a teburin Firimiya a kakar wasa ta 1928 zuwa 29.

A shekarar 1884 ne dai aka kafa kungiyar amma a wancan lokacin ana kiran ta ne da sunan Leicester Foxes.

Sau hudu Leicester ke zuwa matsayin na biyu a gasar FA, wacce ta kasance kungiyar da aka fi yawan doke wa a wasan karshe a tarihin gasar ta FA.

Amma yanzu ta shiga sahun kungiyoyin da ke barazana ga manyan kungiyoyi a Ingila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.