Morocco
Mutane Biyu sun Mutu Wajen Kwallon Kafa a Morocco
A kasar Morocco mutane biyu suka mutu, wasu 51 suka jikkata sakamakon yamutsi daya barke a wajen wasan kwallon kafa a birnin Rabat.
Wallafawa ranar:
Talla
Kafofin samun labarai sunce an lalata motoci 11 da aka ajiye a gefen filin wasan kwallon kafan.
Bayanai na nuna kungiyar wasa ta Raja de Casablanca ke wasa a gida da club din Chabab Rif Al Hoceima daga arewacin Morocco a lokacin da tarzoma ta barke.
An tashi wasan biyu da daya a filin wasa na Mohammed na biyar inda club din da tayi wasa a gida ta yi nasara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu