Isa ga babban shafi
Wasanni

Ni na fi dace wa na shugabanci FIFA-Platini

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai, Michel Platini ya bayyana cewa shi ne mutumin da ya fi dace wa ya shugabanci hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai, Michel Platini.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai, Michel Platini. AFP PHOTO / FABRICE COFFRINI
Talla

Platini ya fadi haka ne duk da zarge zargen da ake masa na cewa yana da hannu a badakalar cin hanci da rashawa da ta addabi hukumar ta FIFA.

Platini dai na cikin mutane bakwai da aka bayyana su a matsayin wadanda ke son dare wa kan kujerar shugabancin hukumar FIFA bayan zaben da za a gudanar a shekara mai zuwa .

A cewarsa kwarewar da ya ke da shi a matsayinsa na tsohon dan wasa kuma mai horar wa, da kuma dabarun da ya ke da shi na iya gudanarwa, ya zarce na sauran mutanen shida da ke neman shugabancin na FIFA.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.