Isa ga babban shafi
FIFA

Mutane 8 ke takarar shugabancin FIFA

Mutane takwas ne suka bayyana kudirin tsayawa takarar zaben shugabancin Hukumar kwallo kafa ta duniya FIFA domin maye gurbin Sepp Blatter. A daren jiya ne wa’adin bayyana kudirin takarar ya cika, kuma idan an jima ne a yau Talata ake sa ran FIFA za ta fitar da sunayen ‘Yan takarar a hukumance.

'Yan takaraar neman kujerar shugabancin FIFA David Nakhid da Michel Platini da Ali ben Al Hussein da Musa Bility da Tokyo Sexwale da Jérôme Champagne da Salman bin Ibrahim Al Khalifa, Gianni Infantino
'Yan takaraar neman kujerar shugabancin FIFA David Nakhid da Michel Platini da Ali ben Al Hussein da Musa Bility da Tokyo Sexwale da Jérôme Champagne da Salman bin Ibrahim Al Khalifa, Gianni Infantino Reuters & AFP - Montage RFI
Talla

A jiya Litinin shugaban hukumar kwallon yankin Asiya Shiekh Salman bin Ibrahim al Khalifa na Bahrain da sakataren hukumar kwallon kafa ta Turai Gianni Infatino suka bayyana aniyarsu ta shiga takarar zaben na FIFA.

Ana ganin takarar Infatino barazana ce ga Platini wanda FIFA ta dakatar tsawon watanni uku.

Daga cikin mutane 8 din da suka fito takara akwai Yariman Jordan Ali Bin Al Hussian dan uwa ga Sarki Abdallah na Jordan wanda ya kalubalanci Blatter a zaben da aka gudanar a bana.

Sannan akwai Michel Platini na Faransa toshon fitattcen dan wasan kwallon kafa kuma shugaban hukumar kwallon kada ta Turai.

Sai dai yanzu haka an dakatar da Platini daga harakar kwallo na tsawon kwanaki 90 har sai FIFA ta kammala binciken wata badakalar kudin kwangila kimanin euro miliyan guda da dubu dari takwas da ake zargin shugaban kwallon na Turai.

Akwai Jerome Champagne na Faransa kuma mataimakin sakatare Janar na hukumar FIFA a zamanin Blatter.

Champagne dai duk da cewa ba dan kwallo ba ne amma dan jarida ne da ke sharhi akan kwallon kafa a wata mujjalar wasanni a Faransa.

Akwai David Nakhid na Trinidad da Tobago, wanda ya shiga takarar da nufin ganin shiugabancin hukumar FIFA ya fice daga Turai.

Akwai Tokyo Sexwale Dan kasar Afrika ta kudu wanda ya bayyana kudirin takararsa a ranar Asabar. Sexwale dai yana cikin wadanda aka daure a gidan yari tare da Nelson Mandela. Kuma yana cikin mambobin kwamitin da suka shirya gasar cin kofin duniya da Afrika ta kudu ta karfi bakunci a 2010

Akwai kuma Musa Bility shugaban hukumar kwallo kafa a Liberia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.