Isa ga babban shafi
Tennis

Anderson ya yi waje da Murray a US Open

A kwanaki na 8 a gasar US Open da ake gudanarwa a Amurka, Kevin Anderson na Afrika ta kudu ya kai zagayen kwata fainal a bayan ya yi waje da Andy Murray na Birtaniya a ranar litinin.

Andy Murray na Birtaniya ta sha kashi a US Open
Andy Murray na Birtaniya ta sha kashi a US Open AFP/AFP
Talla

Stan Wawrinka wanda ya lashe Rolland Garros a Faransa ya yi waje ne da Donald Young na Amurka.

Haka ma Roger Federer na Switzerland ya tsallake zuwa kwata fainal bayan ya doke John Isner, zai hadu ne kuma da Richard Gasquet na Faransa.
A bangren mata

Petra Kvitova ta tsallake zagayen kwata fainal, haka ma Victoria Azerenka ta Belarus ta kai zagayen Kwata fainal bayan ta doke Varvara Lepchenko ta Amurka ci 6-3 da 6-4.

Serena Williams za ta hadu ne da yayarta Venus Williams a yau Talata bayan ta doke Madison Keys ta Amurka.

Serena na neman kafa tarihi ne a bana idan har ta lashe US Open, domin zai kasance ta lashe dukkanin manyan gasannin Tennis a duniya da suka hada da Australian Open da Rolland Garros ta Faransa da Wimbledon a Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.