Isa ga babban shafi
wasanni

Wawrinka ya lashe kofin gasar Roland-Garros

A kwallon Tennis jiya lahadi ne Stanislas Wawrinka dan kasar Swiss ya yi nasarar daukar kofin gasar French Open ko kuma Roland Garros bayan ya doke abokin karawarsa Novak Djokovic dan kasar Sabiya.

Zakaran Roland-Garros, Stan Wawrinka dauke da kofin shekara ta 2015.
Zakaran Roland-Garros, Stan Wawrinka dauke da kofin shekara ta 2015. RFI/ Pierre René-Worms
Talla

Wannan ne dai karo na farko da Wawrinka ke daukar kofi a gasar ta Roland Garros, kuma kofi na biyu da ya taba dauka a manyan wasannin Tennis na duniya, domin kuwa a shekarar bara ya yi nasarar daukar irin wannan kofi a gasar Australian Open.

Nasarar da wawrinka mai shekaru 30 a duniya ya yi a jiya lahadi, ta ba shi damar kasance a cikin manyan ‘yan wasan Tennis na duniya, kamar Roger Federer wanda ya dauki kofuna 17, Rafael Nadal sau 14, Novak Djokovic kofuna 8, sai Andy Murray mai kofuna biyu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.