Isa ga babban shafi
Najeriya

Yarjejeniyar Adidas da Najeriya ta kawo karshe

Kamfanin Adidas da ke samar da tufafin wasanni ya yi gargadin kai Najeriya kotu idan har ‘Yan wasan kasar suka yi amfani da tufafin kamfanin a farkon shekara ta 2015. Shugaban hukumar kwallon Najeriya Amaju yace kamfanin ya rubuto a hukumance cewa zai kawo karshen yarjejeniyarsa da Najeriya a karshen wannan shekarar ta 2014.

Kamfanin Adidas mai samar da tufafin wasanni
Kamfanin Adidas mai samar da tufafin wasanni REUTERS
Talla

Akan haka kuma shugaban kwallon Najeriya yace za su daina amfani da kayan Adidas don gudun kada kamfanin ya kai Najeriya kotu.

A cewar Amaju suna ci gaba neman kulla yarjejeniya da wasu kamfanonin da ke samar da tufafin wasannin don gudun fuskantar matsala da Adidas.

Bayanai dai na cewa kamfanin na Adidas yana son kawo karshen yarjejeniyarsa da Najeriya ne bayan kasar ta kasa tsallakewa zuwa gasar cin kofin Afrika da za a gusdanar a kasar Equatorial Guinea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.