Isa ga babban shafi
Wasanni

An fitar da Najeriya da Aljeriya daga wasan Brazil

A ci gaba da karawa a gasar neman kofin duniya na kwallon kafa da ke gudana yanzu haka a kasar Brazil, a yanzu dai Faransa da Jamus sun samu nasarar tsallakewa zuwa zagayen da ke biyewa na kusa da na karshe wato Quarter finals bayan da Faransa ta doke Najeriya sannan kuma Aljeriya ta sha kashi a hannun kasar Jamus.

kwallon Najeriya da Faransa a Brazil
kwallon Najeriya da Faransa a Brazil REUTERS/David Gray
Talla

Da farko dai an soma karawa ne tsakanin Najeriya da kuma Faransa, inda aka tashi wasan ci 2 da nema, wato Faransa na da galaba, duk da cewa sai da aka share kusan mituna 80 ana karawa kafin faransawan sun sanya kwallonsu ta farko a ragar Najeriya, kuma wani dan wasa mai suna Paul Pogba ne dan asalin kasar Togo ya zura kwallo ta farko.
A daidai lokacin da aka shiga mintuna na cis’in da daya ne wani dan wasan Najeriya mai suna Josheph Yobo ya zura kwallo a ragarsu, hakan ya sa aka tashi wasan ci biyu da nema kenan, wato Faransa ta yi nasarar zuwa zagaye na gaba.
Sai kuma wasa na biyu da aka buga a cikin daren jiya tsakanin Aljeriya da kuma kasar Jamus, inda aka tashi wasan Jamus na da ci 2 yayin da Aljeriya ke da ci daya. An dai share tsawon mintuna cis’in ana fafatawa ba wanda ya zura kwallo a ragar wani, to sai dai bayan da aka yi karin lokaci, ‘yan wasan na Jamus sun samu nasarar jefa kwalloye 2 a ragar Algeria, kafin daga bisani Algeria ta rama ci daya.

Shi kuwa mai horas da ‘yan wasa na Najeriya Stephen Keshi wanda ke zantawa da menama labarai jim kadan bayan kammala wasan, ya zargi alkalin da ya hura wannan wasa mai suna Mark Geiger dan asalin kasar Amurka, da tafka kura-kurai a cikin aikinsa.

To a can Algeria kuwa duk duk da kashin da ‘yan wasansu suka sha, amma an share tsawon daren jiya ana gudanar da bukukuwan domin jinjinawa ‘yan wasan a birnin Algers, yayin da aka samu barkewar tarzoma a birnin Lyon na kasar Faransa sakamakon yadda wasu ‘yan Algeria mazauna Faransa suka fantsama kan tituna suna zanga-zangar har ma da kone-kone bayan kammala wasan.
Bayan nasarar da suka sama a wasanninsu na jiya, a yanzu dai Faransa za ta kara ne da kasar Jamus a zagayen quarter Finals a ranar juma’a mai zuwa, yayin da a marecen yau talata Argentina za ta kara da kasar Switzerland sannan kuma Amurka ta fafata da kasar Belgium domin neman zuwa zagayen quarter finals.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.