Isa ga babban shafi
Ingila

FA: An hada City da Chelsea, Arsenal da Liverpool

An hada manyan kungiyoyin kwallon kafa su kashe kansu a zagaye na biyar a gasar FA ta Ingila a jiya lahad Inda aka hada Chelsea wasa da Manchester City kungiyoyin da ke harin lashe kofin Premier a bana.

Kocin Chelsea  José Mourinho.
Kocin Chelsea José Mourinho. REUTERS/Andrea Comas
Talla

A daya bangaren kuma an Hada Arsenal da ke jagorancin Teburin Premier wasa da Liverpool a zagaye na biyar inda za’a tantance ‘Yan wasa 8 da zasu tsallake zuwa zagayen Kwata Fainal.

A tsakiyar watan gobe mai kamawa ne za’a yi wannan fafatawar tsakanin manyan kungiyoyin guda hudu.

A watan Nuwamba, Arsenal ta doke Liverpool ci 2-0 kuma kungiyoin biyu zasu fara kece raini a Anfield ne a league kafin makon da zasu sake fafatawa a FA a filin wasa na Emirates.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.