Mikel da Yaya Toure da Drogba ke takarar gwarzon Afrika a bana
Hukumar da ke kula da sha'anin Kwallon kafa a Afrika CAF ta ware sunan John Obi Mikel na Najeriya da Yaya Toure da Didier Drogba na Cote d'Ivoire a matsayin wadanda za'a zabi Gwarzon Afrika a bana.
Wallafawa ranar:
Yaya Toure mai shekaru 30 da ke taka kwallo a Kungiyar Manchester City yana neman lashe kyautar ne karo na uku a jere, bayan ya lashe kyautar a 2011 da 2012.
Didier Drogba, ma da ke taka leda a kungiyar Galatasaray ta Turkiya, ya taba lashe kyautar har sau biyu a shekarar 2006 da 2009.
Wannan ne kuma karon farko da aka zabi Mikel Obi cikin ‘yan wasa uku da za’a zaba gwarzon Afrika. Inda wasu masoya kwallon kafa a Afrika ke ganin ya dace ace Dan Najeriya ya lashe kyautar a bana saboda John Mikel Obi ne ya jagorancin tawagar Super Eagle da suka lashe kofin Afrika a kasar Afrika ta Kudu.
A ranar 9 ga watan Janairu ne za’a bayyana sunan wanda ya lashe kyautar gwarzon na Afrika a birnin Lagos.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu