Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Na yi kuskure wajen zabin ‘yan wasa na- Maurinho

Mai horar da ‘yan wasan Chelsea Jose Maurinho ya amsa yin kuskure wajen zabin ‘yan wasansa da suka kara da Basel a jiya inda aka doke Chelsin da ci 1-0 a gasar zakarun nahiyar turai.

Kocin Chelsea Jose Mourinho
Kocin Chelsea Jose Mourinho REUTERS/Suzanne Plunkett
Talla

Duk da cewa ta tsallaka zuwa zagaye na gaba, Itama Barcelona ta sha mamaya a hanun Ajax ta kasar Holland da ci 2-1.

Yanzu Ajax na matsayi na uku a rukuninsu na H ganin cewa AC Milan ta doke Celtic da ci 3-0, Ajax kuma a yanzu haka na bukatar ta doke AC Milan idan suka hadu a wasansu na gaba.

To itama Borussia Dortmund tsallaka zagaye na gaba a gasar bayan doke Napoli da ci 3-1.

Wannan nasara da Dortmund ta samu tamkar daukan fansa ce akan Napoli wacce ta doke ta a watan Satumba da ci 2-1.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga a gasar, Zenit Saint Petersburg da Athletico Madrid sun ta shi da ci 1-1, Bucharest da Schalke 04 sun ta shi canjaras yayin da FC Porto da Austria Vienna suka ta shi suma da ci 1-1.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.