Isa ga babban shafi
CAF

CAN 2013: Carthage Eagles na Tunisia

Kasar Tunisia tana daga cikin manya kasashen da ake hasashen za su taka rawar gani a Gasar cin kofin Afrika a bana, domin sau 15 ne kasar ke haskwa, kuma ta taba lashe kofin gasar a 2004 tare da zuwa matsayi na biyu da na uku da na hudu a lukutta da dama.

Tambarin 'Yan wasan Carthage Eagles na Tunisia
Tambarin 'Yan wasan Carthage Eagles na Tunisia
Talla

Cikin tawagar Carthage Eagles na Tunisia akwai matashin dan wasa Youssef Msakni na kungiyar Esperence wanda al’ummar kasar suke kira da sunan Messi

A ajin matsayi, Tunisia ita ce kasa ta 8 a Afrika amma kasa ta 45 a Duniya.

A baya bayan nan Tunsia ta doke Habasha ci 4-0, amma ta sha kashi hannun Kamaru ci 3-0 tare da sake shan kashi a hannun Guinea ci 3-0.

A bana kuma an hada Tunsia rukuni daya ne da Cote d’Voire da Algeria da kuma kasar Togo, rukunin da ake ganin zai fi sauran rukunonin zafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.