Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Messi da Ronaldo da Iniesta zasu yi takarar kyautar gwarzon duniya.

Hukumar kwallon kafar Duniya ta FIFA ta fitar da sunayen Lionel Messi da Cristiano Ronaldo da kuma Andres Iniesta a matsayin ‘Yan wasan da za su yi takarar lashe kyautar Ballon D’ Or, wato dan wasan da ya fi kowa iya taka kwallo a duniya.

Ronaldo (Hagu) Messi (Tsakiya) da iniesta (Dama)
Ronaldo (Hagu) Messi (Tsakiya) da iniesta (Dama) i2.cdn.turner.com
Talla

Dayawa dai na ganin cewa kyautar zata tsaya ne a tsakanin Messi da Ronaldo.

Messi dan shekaru 25, sau uku yana lashe wannan kyauta, dayawa kuma har ila yau, na kyautata zaton akwai yiwuwar ya sake lashe kyautar. Shi dai Ronaldo sau biyu yana lashewa.

A kakar wasan da ta gabata Ronaldo dai ya zira kwallaye 46 ne a yayin da Messi ya zira kwallaye 50.

A ran bakwai ga watan Janairun shekara mai zuwa ne za a bada kyautar bayan ‘Yan jarida, kyaftin- Kyfatin na club daban daban da kuma masu horara da ‘Yan wasa sun yi kada kuri’unsua birnin Zurich dake kasar Switzerland.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.