Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

CAF ta kori Etoile Sahel daga gasar zakarun Afrika

Hukumar kwallo kafan nahiyar Afrika, ta kori club din kasar Tunisia, ta Etoile Sahel, daga cikin gasar cin kofin zakarun nahiyar Afrika na wannan shekara.

Tambarin hukumar gasar wasan CAF
Tambarin hukumar gasar wasan CAF
Talla

An dai kori club din ne, domin abkawa filin wasa da magoya bayanta su ka yi sau biyu a yayin da su ke wasan cikin gida da club din Esperance a wannan watan, inda su ka yi ta hurga kayayyakin wuta, duwatsu da kuma kwalabe a lokacin da su ka ga, Esperance ta zira kwallaye biyu a ragarsu.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP, ya ruwaito cewa hakan ya sa alkalin wasan ya tsai da wasan a cikin minti na 69.

A na dai ganin wannan hukunci zai sa masu sharhi akan kwallon kafa su jinjinawa hukumar, domin a da ana zargin ita hukumar, da yin sassauci ga club masu kawo tashin hankali a lokacin wasanni.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.