Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Tottenham ta kammala cinikin Adebayor

Kungiyar Tottenham tace Emmanuel Adebayor ya kulla yarjejeniya da ita daga Manchester City bayan bayar da aron dan wasan a bara inda ya zira kwallaye 18 a wasanni 37 da ya bugawa Tottenham. Babu wani bayani game da cinikin dan wasan ba amma kafafin yada labaran Birtaniya sun ruwaito kungiyar ta saye dan wasan ne akan kudi da suka tasan ma Fam Miliyan Biyar.

Emmanuel Adebayor dan kasar Togo Sanye da rigar kungiyar Tottenham.
Emmanuel Adebayor dan kasar Togo Sanye da rigar kungiyar Tottenham. REUTERS/Philip Brown
Talla

Adebayor yanzu shi ne mutum na uku da kocin Tottenham Andre Villas-Boas ya saya.

Kungiyar Norwich City kuma ta kammala cinikin dan kasar Kamaru Sebastien Bassong daga kungiyar Tottenham.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.