Isa ga babban shafi
Euro 2012

Euro 2012: Jamus da Girka za su kece raini

Akwai karon batta tsakanin Jamus da Girka a yau Juma’a, Inda kasashen biyu za su kece raini tare da huce hushin juna game da matsalar tattalin arzikin kasashen Turai.

'Yan wasan Jamus Ozil da Gomez, suna Tabewa
'Yan wasan Jamus Ozil da Gomez, suna Tabewa REUTERS/David Mdzinarishvili
Talla

Rahotanni sun ce shugabar gwamnatin Jamus Anglea Merkel da ke taka muhimmiyar rawa wajen matsawa kasar Girka aiwatar da matakan tsuke bakin aljuhu, zata kai ziyara Poland domin kallon ‘Yan wasanta.

A yau ne dai Angela Markel zata gana da shugabannin kasashen Italiya da Spain da Faransa a birnin Rome domin ci gaba da tattauna hanyoyin warware rikicin euro, daga Rome ne kuma shugabar za ta mika zuwa Poland domin kallon wasan Jamus da Girka.

Ziyarar Merkel na zuwa ne a dai dai lokacin da Gwamnatin Bitaniya ke cewa za ta kauracewa wasannin Ingila a Ukraine.

A Tarihi dai, Girka ba ta da nasara akan Jamus a wasanni Takwas da kasashen Biyu suka buga. Domin Sau uku ne kasar Jamus ke lashe kofin Turai, tare da zuwa matsayi na biyu sau uku.

A gasar cin kofin Duniya kuma Jamus sau uku tana lashe kofin.

Kasar Girka ta lashe kofin Turai sau daya kacal a shekarar 2004, tare da zuwa gasar cin kofin Duniya sau biyu.

Idan aka kwatanta martabar kwallon kafa tsakanin kasashen Biyu, gasar Bundesliga da ake gudanarwa a Jamus ta fi gasar Girka Martaba Domin kungiyoyin Jamus sun lashe gasar cin kofin zakarun Turai sau Shida tare da zuwa matsayi na biyu sau Tara.

Amma Sau daya ne wata kungiya daga Grika ta buga wasan karshe ba tare da lashe kofin ba.

Portugul dai zata kara ne da Jamus ko Girka a zagayen kusa da karshe

Amma Tun fara gasar Turai ne shugaban EUFA Michel Platini ya yi hasashen kasar Jamus da Spain ne za su buga wasan karshe saboda gamsuwa da shirin su da kuma tarin zaratan ‘Yan wasan su.

Sai dai kocin Jamus yace shi yana ganin kasar Spain ce zata lashe kofin gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.