Isa ga babban shafi
Olympics

Gebrselassie ba zai haska ba a London

Fitaccen dan gudun famfalaki, Haile Gebrselassie dan kasar Habasha ba zai haskawa ba a wasannin Olympics bayan zuwa matsayi na Bakwai a tseren gudun mita 10,000 a wasannin Fanny Blankers-Koen da aka gudanar a kasar Holland.

Haile Gebrselassie a lokacin ya lashe gasar Marathon a birnin New York
Haile Gebrselassie a lokacin ya lashe gasar Marathon a birnin New York Reuters/Ray Stubblebine
Talla

Gebrselassie mai shekaru 39 na haihuwa yazo na biyu ne da dakikoki 9 tsakanin shi da abokin karawar shi Tariku Bekele wanda wannan ne kuma wasannin tantance wanda zai wakilci Habasha a birnin London.

Bayan kammala wasannin, Gebreselassie yace gurin shi na zuwa Olympic ya kawo karshe.

Gebreselassie dai ya nemi fatar wakiltar Habasha wasannin Olympic karo na biyar, bayan ya lashe kyautar Zinari su biyu a wasannin da aka gudanar a shekarar 1996 da 2000.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.