Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

AC Milan ta fasa sayen Tevez

AC Milan ta dakatar da bukatarta na sayen Carlos Tevez na Manchester City, bayan Alexander Pato ya yi watsi da komawa PSG a Faransa.Kamfanin dillacin labaran Ansa a kasar Italiya ya ruwaito cewa ana cikin tattaunawa ne tsakanin Adriano shugaban Milan da Manchester city da kuma kuma wakilin Tavez, sai ga labarin Pato ya fasa komawa PSG.

Carlos Tevez dan wasan Manchester City
Carlos Tevez dan wasan Manchester City AFP
Talla

Kasancewar Pato a Milan ne dai yasa kungiyar watsi da bukatar neman Tevez.
Tun da farko dai kafofin yada labaran kasar Italia sun ruwaito shugaban Milan ya kai ziyara ingila domin kawo karshen cinikin Tevez.

A Faransa ma kafofin yada labaran kasar sun ruwaito PSG ta kulla yarjejeniyar kudi Euro milliyan 28 tsakaninta da Pato, amma daga bisani kuma Pato ya yi watsi da bukatar PSG.

A gasar Seria A, wannan batu ne na cinikin ‘yan wasa yasa aka manta da babbar wasa da za’a gudanar tsakanin AC da Inter Milan a ranar Lahadi.

AC Milan dai ta bude hanya ne ga Inter Milan domin mallakar Tevez, al’amarin da zai yi wuya ya faru kafin su kara da juna a ranar Lahadi.

Maki 8 ne tsakanin Inter Milan da AC Milan da ke jagorancin table da Juventus.
Idan dai inter ta sha kashi hannun Milan, hakan zai karye kwarin gwiwar da take da shi.

A daya bangaren kuma Juventus zata yi fatar ganin Inter ta doke Milan domin samun zama a saman Table idan har ta doke Cagliari.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.