Isa ga babban shafi
Wasanni

Juventus ta haye wasan karshe na neman kofin Italiya

Juventus ta samu hayewa zuwa wasan karshe na Kofin Italiya bayan da suka tashi wasa canjaras babu ci tsakaninta da abokiyar hamayyarta Inter Milan a ranar Talata, saboda nasarar da ta yi 2-1 a wasan haduwar farko.

Dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo yayin wasar da suka tashi canjaras da Iner Milan kuma suka haye suka haye wasan karshe na kofin Italiya
Dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo yayin wasar da suka tashi canjaras da Iner Milan kuma suka haye suka haye wasan karshe na kofin Italiya REUTERS/Massimo Pinca
Talla

Tawagar ta Andrea Pirlo za ta fuskanci Napoli ko Atalanta, waɗanda zasu kece raini da yammacin yau, a haduwarsu ta farko dai sunyi canjaras babu wanda ya ci wani.

Rabon Juventus da ta sha duka tun a watan da ya gabata, lokacin da ta sha kashi a hannun Inter da ci 2-0 a gasar Serie A, yayin da kocin kungiyar Pirlo ya ja tawagarsa a gasar ligue da na kofuna duk da ya fara jagorantar kungiyar da tangal-tangal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.