Dokar kulle bazata shafi gasar Primier ba - Boris Johnson
Franministan Birtaniya Boris Johnson yace sabbin matakan sake killace al’ummar kasar bazai shafi wasannin kungiyar kwallon kafa ta Firimiya da sauran nau'ikan fitattun wasannin kwararru a Ingila ba.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A ranar Litinin Boris Johnson yayin jawabi ta kafar talabijin ya sake sanya dokar kulle da zai shafi Kusan mutane miliyan 56 a Ingila, mai yiwa har zuwa tsakiyar watan Fabrairu, domin magance kaifin yaduwar cutar korona da ta sake bulla a karo na biyu.
Matakan, wadanda suka hada da rufe makarantun firamare da sakandare, za su fara aiki yau Laraba, bayan da kasar Scotland ta sanar da makaimaciyar da ta fara aiki tun daren jiya.
To sai dai cikin al’umma da wannan doka ta kebe, harda "fitattun 'yan wasa (da masu horar da su, da kuma iyayen ‘yan wasa ‘yan kasa da shekaru 18.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu