Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo ya harzuka da bai wa Luka zakaran kwallon Turai

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Juventus Massimiliano Allegri ya ce Cristiano Ronaldo ya harzuka matuka da yadda Luka Modric ya doke shi wajen lashe kyautar dan wasa mafi hazaka na nahiyar Turai.

A cewar Kociyan na Ronaldo, dan wasan ya zura kwallaye har 15 a wasannin gasar cin kofin zakarun Turai wanda yakamata a ce UEFA ta yi la'akari da shi wajen bashi kyautar.
A cewar Kociyan na Ronaldo, dan wasan ya zura kwallaye har 15 a wasannin gasar cin kofin zakarun Turai wanda yakamata a ce UEFA ta yi la'akari da shi wajen bashi kyautar. REUTERS/Jorge Silva/File Photo
Talla

A jiya ne dai Modric dan wasan tsakiya na Madrid da Crotia ya doke takwarorinsa Muhammad Salah na Liverpool da Cristiano Ronaldo na Juventus wajen lashe kyautar ta zakaran kwallon nahiyar ta Turai.

A cewar Allegri ba a yi wa Ronaldo adalci ba, duk kuwa da cewa ya zura kwallaye 15 a gasar zakarun Turai ya kuma lashe kofin a bangaren Real Madrid, amma babu abin da za su ce kan hukuncin.

Ronaldon dai shi ne dan wasan gaba mafi hazaka da kungiyoyin ‘yan jaridu da kuma kwaca-kwacai na kungiyoyin kwallon kafar Turai suka zaba la’akari da hazakar da ya nuna a kakar wasan da ta gabata, wanda Allagri ya ce zaben Modric din bai masa dadi ba matuka.

Baya ga kyautar ta zakaran Turai akwai kuma yiwuwar Modric zai shiga jerin wadanda ake saran za su lashe kyautar Ballon D’or da ya kunshi Ronaldon da Lionel Messi wadanda tsawon shekaru suka saba lashe kyautar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.