Isa ga babban shafi
Brazil

An kama Vincezo Macri jigo a safarar hodar ibilis a Duniya

Yan Sandan kasar Brasil sun sanar da capke wani kusa a kungiyar nan ta Mafia ta kasar Italiya da aka jima ana nema .Hakan na a mtsayin babbar nasara ga kasashen dake yaki da safarar hodar ibilis a Duniya.

Hodar ibilis da yan sanda suka kama a Turai
Hodar ibilis da yan sanda suka kama a Turai AFP PHOTO PATRICE COPPEE
Talla

Yan Sanda sun samu kama Vincezo Macri a filin tashi dama saukar jiragen saman birnin Sao Polo dake kudu maso gabacin kasar ta Brazil dauke da takardun jabu na kasar Venezuela da wani suna can daban.

Vicenzo ya yi kauri suna wajen safarar hodar ibilis,inda aka bayyana shi a matsayin wani kusa da ya taka gaggarumar rawa kama daga shekara ta 2004 zuwa 2015 wajen fitar dama shigo da hodar ibilis daga kasashen Morroco, Netherland, tsibirin Dominicain zuwa Italiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.