Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Maina Bukar: Kalubalen da ke gaban Macron bayan samun nasara

Wallafawa ranar:

Bayan Emmanuel Macron ya lashe zaben Faransa da aka gudanar zagaye na biyu a ranar Lahadi, masu sharhi na ganin tarin kalubalen da ke gabansa ne za su mamaye nasarar da ya samu. Wannan ne karon farko cikin shekaru 60 da aka gudanar da zaben Faransa zagaye na biyu ba tare da ‘yan takarar manyan jam’iyyun siyasar kasar guda biyu ba, wato Republican da Socialist. Samun rinjaye a Majalisa ne yanzu babban kalubalen da ke gaban Macron, wanda ya kaddamar da siyasar jam’iyyarsa a cikin shekara guda. Dangane da wannan, Awwal Janyau ya tattauna da Maina Bukar Karte na Jami’ar Birnin Yamai a Jamhuriyyar Nijar.  

Zababben shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron.
Zababben shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron. REUTERS/Francois Mori
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.